Uncategorized

Allah sarki cikin Tausayi Abdullahi Amdaz yayi wani jawabin akan saratu Gidado daso bayan sakon Rasuwarta ya isa gareshi😭

Lallai mutuwar Daso abar tunawa ce, kuma Babban abinda nake tunawa game da wannan baiwar Allah shi ne, girmama alkawari da kokarin sauke nauyin da yake kanta.

Duk lokacin da nayi mata rubutun proposal ko wani project, bata gushewa saita biyani hakkina akan lokaci, sannan idan mukayi Alkawari karfe 10am na safe, zatazo tun karfe 9:45am, zata jirani tsawon mintuna 15 da sun cika da minti biyar, zata tafi saidai ta kirani a waya, tace Amdaz sai gobe kamar lokacin da muka tsara.

Hakika cika Alkawari siffar mutumin kirkice, muna miki Addu’ar Allah yayi miki Rahma ya yafe miki kuskurenki, ya azurtaki da Aljannarsa Albarkacin Ibadar wannan wata mai albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button